Wata Dalibar Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria Ta Yi Yunkurin Halaka Kanta

Daliba mai suna Nafisa ‘yar aji biyu a jami’ar ABU Zaria, a bangaren karatun kimiyar komfuta, ta so kashe kanta saboda damuwa, kamar yadda ake zargi kuma kamar yadda za ku iya gani a wadannan hotuna na kasa.

Idan ba mu mance ba, kwanakin baya haka wani dalibin ABU cikin azumin da ya wuce ya kashe kansa. Haka ma bara wata dalibar ‘yar aji uku a ABU, mai suna Aisha Abdul, ta kashe kanta har ta bar wasika da take nuna cewar iyayenta ne take tuhuma musammar uwarta.
Haka zalika shekaru biyu da suka wuce wani dalibin jam’iar ATBU ya rataye kansa.

Ko me ya sa kisan kai ya yi yawa ne a tsakanin dalibai a ‘yan shekarun nan?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.