An Kama Malamin Tsibbun Dake Yi Wa ‘Yan Siyasa Sihiri A Jihar Zamfara

A jiya Asabar 6-7-2019 asirin wani matsubbuci da ke yi wa ‘yan siyasa tsaface-tsaface da sunan neman mulki ta batacciyar hanya da kuma toshe bakin jami’an hukumar EFCC kar su yi aikin su kamar yadda ya dace ya fara tonuwa a jihar Zamfara.

Shi dai wanda aka kama mai suna LAWALI DAWAI daga karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, ya shiga komar jami’an tsaron farin kaya ne, bayan sun bi diddikinsa, tare da biyar wayar da ya ke yi, inda suka nemi zai yi masu aiki, bayan sun kama shi ne, su ka yi masa bincike-bincike musamman a wayoyinsa , inda su ka ga bayanai na aika-aikar da ya ke yi da. Wanda nan take ya tabbatar da cewa akwai wani aiki da aka sanya shi na neman rufe bakin wannan Gwamnatin akan binciken da hukumar EFCC ta fara yi akan tuhumar yadda aka yi wasu ayukka a Gwamnatin da ta shude, duk da dai har yanzu akwai bayanai na irin turbude-turbuden da su ke yi. Wanda zuwa yanzu bai yi cikakken bayani ba.

Amma dai ya tabbatar da cewa akwai wata tukunya da ya yi wasu ayukka, akan EFFC wadda ya turbude a tsakanin Gusau da Bungudu a cikin jeji. Wanda jami’an tsaro su ka jagoranci zuwa a tono ta. Kamar yadda kuka gani a wadannan hotuna.

Yanzu dai an mika shi ga jami’an tsaro domin tatsar bayanai akan masu sanya shi aikin, da kuma irin aikace-aikacen da ya yi a baya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.