Yadda aka boye Magajin Garin Daura a jihar Kano

 

A safiyar yau Talata ne jami’an tsaron Najeriya karkashin jagoracin CP Abba Kyari da hadin gwiwar abokan aikin sa dake nan jihar Kano suka gano inda masu garkuwa da mutane suka boye Magajin Garin Daura Musa Umar, wanda yake tsare a wajen su kimanin wata biyu.

Yadda abun ya faru shi ne tun yammacin jiya Litinin zuwa wayewar garin yau Talata ne jami’an tsaron Najeriya suka yiwa yakin Unguwar Samaigu kan Titin Madobi karamar hukumar Kumbotso kusa da Sani Abacha Youth Center tsinke tare da musayar wuta, sakamakon gano gidan da masu garkuwa da mutane suka boye Magajin Garin Daura Alh. Musa Umar a nan jihar Kano, Wanda daga bisani cikin ikon Allah Ta’ala jami’an tsaron suka yi nasarar kubutar da shi inda yanzu ya shaki iskar ‘yanci.

Kuma tun daran jiya aka yi nasarar kama mutum biyu daga cikin masu garkuwar a safiyar yau kuma lokacin da aka yi wata musayar wuta da jami’an tsaron suka harbe mutum daya dukkan nin su kuma Fulani ne, babban abun takaicin shi ne inda su masu garuwar suka shigo cikin mutane suka kama gidan haya lamarin da yasa mutane da dama suka tofa albarkacin bakin su kan wannan lamarin musamman yadda ake bawa mutane gidajan haya ba tare da yin bincike ba, kuma daman tun kwanakin baya ake ta yada rade-radin cewar masu garkuwa da mutanan sun bazamo wasu jihohin nan arewa ciki har da nan kana ya kamata dai al’umma a yi taka tsantsan kuma a lura da kau.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne mutanen garin Daura suka yi addu’o’i domin Allah ya kubutar da Magajin Gari Umaru.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.