Senata Ya Kirawa Kansa Ruwa

 

Senata mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya Senator Elisha Abbo, na cigaba da shan matsin lamba daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da daidaikun jama’a akan ya gaggauta yin murabus daga kujerar sa, a gefe guda kuma wasu kungiyoyin na cigaba da kiran majalisar dattawa ta ladabtar da Senatan, yayinda wasu kuma ke kira da a kori Senatan saboda abunda suka kira rashin dattakun senatan.

Wannan kiraye-kirayen na zuwa ne biyo bayan wani faifan Bidiyon da ya nuna Senatan da yan shamiyar sa ciki hada dogarin sa, suna dukar wata ma’aikaciyar wani shago a birnin tarayya Abuja.

Wannnan bidiyo da na’urar CCTV ta shagon ta nada, ya janyowa Senatan cakwakiya domin kawo yanzu kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya wato Amnesty International a turance, tayi kira ga majalisar dattawa da kuma jami’an tsaro su gaggauta bincikar lamarin tare da daukar matakin da ya dace.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: