A Jihar Kebbi, An Kama Wasu Da Ake Kyautata Zaton ‘Yan Luwadi Ne, Wasu Manya Na Kokarin Belin Su A Sirrance.

 

Wasu majiyoyi wadanda Jaridar Dimokuradiyya, ta sami labari daga garesu, sun bayyana cewa yanzu haka dabi’ar nan ta Luwadi na yaduwa kamar wutar daji a Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar.

Majiyar ta ce yanzu haka da akwai wata Unguwa da ake mata lakabi da sunan wani Tsohon Gwamnan wata Jiha wanda a lokacinsa aka ce an lalata samari da yawa da wannan dabi’a a jiharsa.

Wasu Inyamurai masu Otal a Birnin Kebbi in ji majiyar ta mu, sun fallasa wani matashin da ya kama daki, kuma maimakon su ga wata zukekiyar mace ta shigo, sai su ka ga wani gardi jami’in Gwamnati. Wannan ne ya sa su ka sanar da abin da ke faruwa.

An ce akwai wani Hakimi a Birnin na Kebbi wanda ya sa aka damke wasu da ake zargi da bakar dabi’ar, har aka sami wadansu su ka lallaba yin belinsu. Sai dai Hakimin ya hana a bada belinsu. Ya ce duk mai bukatar belinsu, ba a boye zai yi ba. Ya fito fili ya sanar cewa ya zo belin ‘yan luwadi.

Shin Ya gaskiyar wannan labarin?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *