Jamiyyar Apc Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Jihar Jigawa

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa ta sanar da jamiyyar APC a matsayin wadda ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin jihar 27

Haka kuma jamiyyar ta APC ta lashe kujerun kamsiloli 287 dake fadin jihar nan

Kakakin Hukumar Habibu Yusif Adamu Babura ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse

Yace jamiyyun siyasa 16 ne suka fafata a zaben na kananan hukumomi

Mallam Habibu Yusif Adamu Babura yace masu sa ido daga sassan kasar nan sun sa ido a zaben tare da yabawa da yadda aka gudanar da zaben

Ya kuma bayyana cewar shugabannin hukumomin zabe na jihohin kasar nan 36 sun ziyarci Jigawa domin ganin yadda zaben ya gudana tare da yabawa da yadda aka gudanar da zaben

Tun da farko shugaban Hukumar zabe ta jihar Rivers Mr Rotimi ya yi alkawarin kwaikwayon takwararta ta jihar Jigawa wajen gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Mr Rotimi wanda ya bada tabbaci a lokacin ganawa da manema labarai bayan tawagar shugabannin hukumomin zabe na jihohi sun sa ido a zaben kananan hukumomin jihar nan da aka gudanar a ranar asabar yace tsarin da hukumar zaben ta jihar Jigawa ta yi wajen rabon kayayyakin zabe masu muhimmanci sun birgeshi shi sabanin yadda suke a jihar Rivers

Mr Rotimi ya kara da cewar hukumar zaben jihar tana daukar dogon lokacin kafin rabon kayayyakin zabe masu muhimmanci dsan haka zasu kwaikwayo tsarin Jigawa

Yace zaben Kananan hukumomin Jigawa ya kasance darasi a garesu wanda zasu kwaikwayi tsarin kasancewar zasu gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar nan gaba kadan

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.