An Kama Jami’in Soji Mai Siyarwa Masu Garkuwa Harsashi A Kaduna

 

Hukumar Yansanda reshen Jihar Kaduna sun wawushe wani Jami’in Sojin kasa mai mukamin Las Kofra bayan an zarge shi da siyarwa masu garkuwa da mutane harsashi

Jami’in Sojan, dan kimanin Shekaru 32- a duniya mai suna, Koza Yabiliok Yan sanda sun zarge shi da cefanarwa da Masu garkuwan alburushi, wanda da haka suka addabi Jihar Kadunan tsawon Shekaru.

Jami’in Sojan, Yabiliok, ya bayyana wa manema Labaru cewar yana siyarwa da mai garkuwan ko wane zagayen harsashin nera dari hudu (N400).

Tun da farko shi Jami’in Sojan yana aiki da shashen maaikatar Sojoji dake Jaji, wato Jaji Military Cantonment, kamar yadda majiyar Punch ta wallafa

To sai dai fa Soja, Yabiliok, yace ko kadan bai yi tunanin mai garkuwa bane, ya dai bayyana mishi cewar suna kokarin kare kan su ne saboda barayin Shanu, shi yasa na siyar mishi.

A nashi bangaren lokacin da yake tattaunawa da manema Labaru Kwamishinan Yansanda Jihar Kadunan,Ali Aji-Janga, ya ce akwai a kalla Mutane 61 suka kama da laifuka da dama da suka hadar da Sanata mutane da Fashi da makami da sauran su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: