Ƙungiyar mawaƙan jam’iyyar (APC) na tuhumar Dauda Kahutu Rarara tare da wasu mutune bakwai da zargin kashe kuɗaɗen ƙungiyar ba bisa ƙa’ida ba.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito a wannan rana, ƙungiyar ta bukaci Rarara tare da sauran waɗanda ta ke tuhuma da su je gaban kwamitin bincike da ƙungiyar ta kafa su amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake musu nan da ɗan wani lokaci.