Babu Batun Bincikar Matar Marigayi Ado Bayero, Da Matar Sarki Sunusi Na II~ Hukamar yaki da rashawa

 

An karyata zargin da jama’a keyi na cewa, hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano zata gayyaci matar mai martaba sarkin Kano don amsa wasu tambayoyi kan zargin da aka yiwa mijinta.

Hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano ita ta bayyana hakan, cikin wata takarda dauke da sa hannun daraktan karbar korafe korafe da sasanta al’umma na hukumar.

Takardar ta bayyana cewa, hukumar bata da masaniya kan wani mutum da ta aika masa da takardar gayyata, cewa bashi da lafiya. Sai dai ta karbi takarda dake nuni da tafiya wajen jinya da babu wata shaida ta wani Asibiti a nan Najeriya, Sannnan Babu wata alama da zata nuna amincewar abun da ake ikrari akai.

Sannan hukumar na zargin masaruatar Kano, sakamakon rashin bayanai karara kan hanyar da aka cire kudaden da ake zargi, sakamakon rashin hadin Kai da Masarautar ke nunawa hukumar domin samar da sahihan bayanai.

Sakamakon hakan, hukumar ta yanke shawarar janye gayyatar farko ta ranar 17 ga watan Yuni 2019, tare da bukatar Masarautar ta basu bayanan da suke nema bisa kundin tsarin hukumar sashe na 31 Kamar yadda akayi kwaskwarima a shekarar 2008 .

Hukumar ta bukaci a mika takardar tallafin jinya da aka bawa kowa ake magana akanta daga cikin kudin in har Akwaita.

Sannan ta umarci a hada da shaidar kwanciya a Asibitin dake kasar wajen, domin baiwa hukumar damar binciken daya dace.

Kazalika Hukumar ta Ce ta lura da wasu Gidajen Jaridar Soshiyal Midiya na Bogi, da ake Amfani da su domin Yada Karya da Kazafi don cimma wata Manufa ta Siyasa.

Duk da Muna da Labarin Irin Dimbin Kudaden da wasu Marasa Kishin Kasa suka Fitar domin Kawai su ga sun Kawo ma Binkicenmu Tasgaro da Yada karya a Kanmu, amma muna Jaddada Musu cewa da Sannu Gaskiya za ta yi Halinta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.