Duk Wanda Ya Sa Hannu A Dokar Wa’azi Ya Yi Ridda – Dr Gumi


Sheikh Gumi yace ” ba dai dai bane gwamnati ta kirkiro doka akan gyare gyare kan addini ba tare da an zauna da Malamai masu ruwa da tsaki daga ko wani bangare ba, wato Malaman Musulunci da na Kirista, Harkan addini ba kamar siyasa bane kuma bai kamata gwamnati ta kunno wutan rikici ba kuma daga baya tazo tana cewa ayi addu’an samun zaman lafiya.

A cewar Shehun Malamin kundin tsarin mulkin kasar mu Najeriya ya ba kowane Dan kasa damar gudanar da addinin da yake so, ba tare da tsangwama ba, batun bada Lasisi babu abin da zai haifar illa matsaloli da samun koma baya, domin a halin da ake ciki da akwai kungiyoyin da su basu yadda da gwamnati ba balle lasisin su.

Inda ya bada misali da kungiyar Boko Haram da ‘Yan Shi’a yace ” waye yabasu lasisi kamin su fara yin wa’azi?” Amma kuma duk da haka suna da magoya baya masu dinbin yawa.

Amma idan har gwamnatin tayi hakan da kyakkyawar manufa wurin inganta harkan karantarwa da koyarwan addini, Allah zai basu nasara a wannan kudiri nasu amma matukar ba hakan ba sanya hannu a wannan kudirin ma kamar ridda ne domin duk wanda ya kange zuwa ga hanya Allah yayi ridda ne.

Kuma a nawa fahimtar gwamnati tayi kuskure wurin gabatar da wannan kudiri domin ba haka ake fuskantar kalubale irin wannan ba,ya kamata a zauna da kowane bangare kuma kowa ya bada nashi gudunmuwar iya fahimtarsa kafin daga bisani gwamnati ta mikawa majalisa domin tabbatar da shi doka.

Dr Gumi ya bayyana cewar ya fara wa’azi tun kafin a kafa wata kungiya, kuma a jihar Kaduna tun a shekarar 2004 lokacin mulkin Obasanjo yake wa’azi , shekaru goma sha biyar kenan yanzu amma babu wanda ya tuntube ni da ire ire na akan wannnan batu saidai kawai muka ji a labarai da jaridu wanda hakan fisabilillahi bai dace ba.

Daga karshe malamin yace idan ance za asa dokar bada lasisi, waye zai ba wani lasisin? Musulmi ne zai ba kirista ko kuwa kirista ne zai ba musulmi?.

Wannan kawai zai rarraba kawunan jama’a ne

Leave a Reply

Your email address will not be published.