Hayaniya ta Dakatar da Wani Alkali a Kotu.

 

RIKICIN DUNIYA.

Wakiliyarmu Zahra Sarki Bauchi

Shari’ar da ke gaban kotun Musulunci dake tudun alkali, cikin garin Bauchi alkalin kotun malam Muhammad Lawal Isma’il, da ke sauraron karar da malam Habu me Nama ya Shigar kan zargin Dan uwan matarsa da laifin boye masa mata har na tsawon watanni goma sha biyu ya Dakatar da Yin Shar’ar.

A cewar mai Kara yabi duk matakan da ya dace ta hanyar waliyai da sauransu don ya ga ya dawo da Matar sa amma Wanda ake Kara ya ki ya barta ta dawo Inji malam Abubakar me Nama.

Ya cigaba da Cewa a Kokarin su na Raba ni da Wannan Matar tawa har yakai ga sun dauko min ‘yansanda mota Guda daga ofishin su da ke Garin Dutsen tanshi da misalin karfe 5 na Asuba Inda suka tursasa ni shiga Motarsu Ko Bari na In Kintsa ba Su yi ba.

Suka hana ni Shiga Gida Kuma gashi Sun san ta bar min Yaro Dan Shekara 4 da Haihuwa duk domin su Wulakanta ni su ci Zarafi na, inji shi.

Bisa Wannan Dalilin yasa na Kawo Karata Gaban Wannan Kotu domin in Samu Adalci mai Dorewa akan Wannan Mutum.

Alkalin Kotun Mai Shari’a Malam Muhammad Lawal Isma’il, ya tambayi matar Bisa Wannan Tuhuma tare da Jan Hankalinta kan cewa ta koma Gidan Mijinta su cigaba da Zaman Aure.

Nan take Matar ta ce Sam Ita ba Za ta koma Gidan sa ba domin Yana Dukanta, Zagin Iyayenta, da Sauran Wulakanci Kala-Kala, Inji ta.

Inda ta ce tana Rokon Kotu, da ta Karba Mata Dan ta da yake Hannun sa domin ta Cigaba da Tarbiyantar da shi.

Alkalin Kotun ya ce Zai tura Wannan Shari’a Gaba Zuwa Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kobi, domin cigaba da Sauraron Wannan Shari’a.

Me za ku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published.