Gazawar Gwamnatin Apc A Bauchi Ita Ta Kawo Mu Kan Karagar Mulki:~ Gwamna Bala Muhammad

 

Wakilinmu Uzairu Bauchi

A wannan Litinin ce 10 ga watan Yunin shekarar 2019, gwamnan jahar Bauchi ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jaha Alhaji Muhammad Sabi’u Baba, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jahar Bauchi Alhaji Abubakar Kari, da mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati dake da ofishi a ofishin mataimakin gwamna jahar, Alhaji Bashir Ya’u.

Yayin rantsar dasu a fadar gwamnatin jahar, gwamna Abdulkadir Muhammad, yayi nuni da cewa, gazawar gwamnatin da ya gada ya sanya al’umma zabarsa a kujerar gwamna, don haka sai ya horesu da suyi aiki tukuru don baiwa marar da kunya.

“Chancartarku, kwarewarku da tarin basirarku ita ta sanya muka baku wadannan mukamai da tunanin zaku taimakawa gwamnati wajen sauke nauyin da aka dora mata na ciyar da jahar dama al’ummar jahar gaba”

Gwamna Abdulkadir, yayi nuni da cewa yanzu gwamnatinsa zata fara aiki gadan gadan don fara cika alkawuran data dauka lokacin yakin neman zabe da ya gudana, sai ya bukaci wadanda aka rantsar da suyi aiki da gaskiya bisa tsarin dokar kasa su kuma kasance masu hakuri tare da nuna biyayya ga jam’iyyar PDP da ta kawosu karagar mulki.

Daga nan sai gwamnan ya gargadesu da cewa suyi hattara da amanar da aka dora musu ta Al’ummar jahar Bauchi.

“Ba an baku mukamai don kuyi amfani da ofishohinku ku azurta kanku bane, mun nadaku don kuyiwa Al’ummar Bauchi aikine, don mu bambamta kanmu da gwamnatin data shude, don haka kuyi aiki bisa rantsuwar da kukayi da Alkur’ani”

Daga nan sai gwamnan ya tayasu murnar samun kansu cikin gwamnatinsa a manyan mukaman gudanar da harkokin mulki da cigaban kowacce gwamnati.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka rantsar, sabon sakataren gwamnatin jahar Bauchi Alhaji Muhammad Sabi’u Baba, yayi alkawarin baiwa marar da kunya tareda yin aiki don nausa jahar Bauchi ga tudun natsira, ba tare da nuna bambanci ba a tsakanin Al’ummar jahar.

Wadanda suka samu halartar taron rantsarwar akwai, sarakunan jahar Bauchi na yanka guda biyar sai wakilin mai martaba sarkin Jama’are, ‘yan majalisun tarayya dana jahohi tare da shugabannin jam’iyyar PDP na jahar da kananan hukumomi 20 na jahar da sauran jigogi a gwamnatin jahar Bauchin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: