
Daga Imam Murtadha
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku bayin Allah masu girma, kun gani, abunda muke ta fada maku, abunda muke ta kokarin ku fahimta, da yake Allah ba azzalumi bane, kuma baya bari ayi zalunci, gashi nan duk abun da muke ta fada, Allah yana ta tabbatar da shi, ba domin komai ba, sai don saboda mu Allah ne a gaban mu, kuma domin sa muke yi, kuma domin karya ta bayyana kowa ya santa, ya fahimce ta, ya gane ta, kuma mun san mu bamu da karfi, bamu da dabara, mun mika wa Allah komai, shi yasa ga shi nan yana ta taimakon mu.
Wallahi, bamu damu ba, duk mai zagi da cin mutunci daga cikin magoya bayan Ganduje yayi tayi, amma mun san cewa, wallahi, daga karshe sai gaskiya tayi halinta.
Har kullum, muna ta addu’o’i, Allah ya dora gaskiya a kan karya, amin. Kai kuwa mai zagi cigaba dayi. Ba dai mun ce Allah ba, ku kuwa sai zagi da ashar, kuci gaba da yi, ga fili ga doki.
Wallahi, bamu taba shaida wa Allah bukatar mu ba ya kunyata mu, kuma muje zuwa, mu dai mun riki Allah kadai!
Yanzu kalli yadda wasu hakimai, bayin Allah, da ke karkashin sabbin masarautun bogi da Gwamna Ganduje wai “ya daga darajar su” suka baro masarautunsu zuwa birnin Kano domin yin Sallar Idi da hawan Sallah, tare da Sarkin gaskiya, Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II. Muna addu’ar, wadannan hakimai Allah ya rufa asirin su duniya da lahira, ya basu abinda suke nema, ya biya masu bukatun su, amin. Hakiman sune kamar haka:
- Dan Isan Kano Hakimin Warawa
- Dokajin Kano Hakimin Garko
- Dan Galadiman Kano Hakimin Bebeji
- Sarkin Shanun Kano, Hakimin Rimin Gado
- Yariman Kano Hakimin Takai
- Barden Kano Hakimin Bichi
- Sarkin Fulanin Ja’idanawa Hakimin Garun Malam
- Makaman Kano Hakimi Wudil
- Sarkin Dawaki Mai Tuta Hakimin Gabasawa
- Dan Kadai Kano Hakimin Tudun Wada
- Dan Madami Hakimin Kiru
- Dan Amar Din Kano Hakimin Doguwa
- Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa
- Matawallen Kano Hakimin Minjibir
- Wakilin Dan Iyan Kano Hakimin D/kudu
- Wakilin Barden Kano Hakimin Gwarzo
- Wakilin Dan Makwayo Hakimin Tsanyawa
- Wakilin Sarkin Yakin Kano Hakimin Ajingi
- Magajin Rafin Kano da sauran su.
Wadannan bayin Allah da suka yi alkawarin kasancewa tare da gaskiya da masu gaskiya, muna rokon Allah yayi masu jagora, ya shirya zuri’ar su, ya kara masu kaunar talakawan su, ya kara masu rufin asiri da sutura duniya da lahira, amin.
Shi kuwa Mai Martaba Sarki, ina rokon Allah yayi masa jagora, ya kara masa hakuri da imani, ya kare shi daga dukkanin sharri da makircin makiyan sa da magautan sa, amin.
Dan uwan ku: