Gwamna Ganduje Ya Bai Wa Sarkin Kano Wa’adi

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Sarkin Kanon Muhammadu Sanusi na biyu wa’adin sa’o’i 48 ya ba da ba’asi akan zargin almubazzaranci da kudin masarauta.

Fadar masarautar Kanon dai ta tabbatar da karbar wasikar neman ba’asin da wa’adin ke kunshe a ciki, amma ta ce za ta nazarcin wasikar kafin daukar mataki na gaba. Sai dai masana shari’a kamar Barrister Audu Bulama Bukarti lauya mai zaman kansa, na cewa “Hukumar ba ta da hurumin binciken Sarki, doka ta ce hukumar ta binciki ma’aikatan gwamnati ne kawai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.