A yau Laraba Mai Martaba Sarkin Gombe Alh. Abubakar Shehu Abubakar III, ya kawo ziyarar gaisuwa ga Mai Girma Gwamnan jihar Gombe Alh. Muhammad Inuwa Yahaya, a fadar Gwamnatin jihar.
Gwamnan ya bawa Mai Martaba Sarkin kan Goron Sallah da ya kawo masa.
Taron ya samu halartar manyan jami’an Gwamnatin jiha da sauran manyan baki.