Sarki Sanusi II Ya Janye Hawan Dorayi Ya Kira Taron Addu’ar Shekara 5 Da Rasuwar Ado Bayero

*Akwai Iyuwar Ganduje Zai Dakatar Da Shi A Gobe

Kana kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya janye hawan Dorayi an maye gurbinsa da yi wa tsohon Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero addu’ar cika shekaru biyar da rasuwa. Tare da addu’ar cikar Sarki Sanusi II shekaru biyar a mulki.

Kazalika Dan jarida Nasiru Salisu Zango ya rubuta a shafinsa na facebook cewa, akwai iyuwar fitar da wata sanarwa a goben dangane da Sarkin.

Lamarin da ya sa wasu rahotanni dake yawo a gari ke hasashen cewa akwai iyuwar a goben Ganduje zai iya bayar da sanarwar dakatar da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Leave a Reply

Your email address will not be published.