Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Soke Hawan Nasarawa

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dakatar da hawan Nassarawa da aka saba yi a duk ranar biyu ga kowacce sallah a Kano.

Wata wasika da aka fitar daga ofishin sakataren gwamnatin Kano aka kuma rarrabawa rundunar ‘yan sandan jihar Kano da hukumar tsaro ta farin kaya, ta bayyana cewar gwamnan Kano zai tunkari wasu muhimman ayyuka wadanda sune suka tilasta dakatar da hawan.

Haka kuma wata majiya ta bayyana cewar akwai wata sanarwar da za ta fito zuwa gobe wacce majiyar mu ke shaida mana cewar ita ma tana da alaka da Mai Martaba sarkin Kano Muhammad Sunusi II.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.