‘Yan Bindiga Sun Arce Da Malamin Katsina Poly

 

A daren jiya ne ‘yan bindiga, wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka sace Dakta Bello Birchi, Malami a Makarantar Kimiyya Da Fasaha ta Hassan Usman Katsina da ke Katsina, a kauyen su da ke Tashar Bara’u da ke karamar Hukumar Kurfi.

Shugaban Kungiyar malaman makarantar Dakta Sabiu ya tabbatar da sace Dr. Bello Birchi, inda ya ce Kungiyar ta damu matuqa kan sace Daya daga cikin yayanta da aka Yi jiya a garin su. Har zuwa yanzu baa samu want labari ba akan shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.