Shugaba Buhari Zai Ziyarci Kasar Saudiyya A Gobe Alhamis

 

In sha Allahu a Gobe Alhamis 30-05-2019 Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla zuwa kasar Saudiyya domin Halartar Babban Taron da kasar ta Saudiyya za ta Jagoranta na kasashen Musulumci na Duniya Organisation of Islamic Cooperation (OIC) a Turance karo na goma sha hudu. (14)

Mai Girma Sarki Salman bin Abdul’aziz Al Sa’ud ne zai Jagoranci Taron wanda Shugabannin kasashen Musulmi na duniya za su halarta wanda za’a fara a ranar Juma’a 31May 2019 dai dai da 26 Ramadan.

Kasarmu Nigeria tana daya daga cikin ‘kasashen da ke cikin kungiyar musulmai ta duniya wanda akan hakan Shugaba Buhari zai Halarta domin Tattaunawa akan Muhimman Batutuwa da suka shafi Musulumci da Kasashen Musulmai.

Muna masa Fatan Alheri, da fatan Allah ya kai mana shi Lafiya, ya dawo mana da shi Gida Lafiya. Amin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.