An Kama Wani Malamin Makarantar Allo Dake Lalata Da Dalibansa Kuma Yake Bada Hayarsu A Yi Lalata Da Su

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto tayi nasarar kama wani malamin makarantar allo mai suna Malam Murtala Mode dake Arkillan Magaji a cikin birnin Sokoto kan zargin sa, da yin lalata da dalibban sa shida.

Da yake bayani ga manema Labarai, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Kaoje, yace a ranar 22, ga watan nan na Mayu, Barrister Hamza Liman na hukumar kare hakkin Bil’adama ta kasa, ya bada rahoton Malamin a ofishin rundunar ‘yan sanda dake a unguwar Arkilla.

A zantawar sa da manema labarai, wanda ake zargin ya bayyana cewa “Ina aikata hakan ne kusan na tsawwon shekaru biyu, kuma ina yine dan kawai in samu kudi”.

Dalibban dake karatu a wajen sa, sun fito ne daga wasu kauyukka dake jihohin Sokoto da kuma Zamfara.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.