Bayan Ritayar Singham: Kano Ta Yi Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda

 

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP M.A Adamu, ya yi umarnin a yi gaggawar turo CP Ahmed Iliyasu zuwa jihar Kano domin zamowa Kwamishinan ‘yan sandan jihar.

Iliyasu ya maye kujerar CP Muhammad Wakili (Singham), wanda ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda a ranar 26 ga watan Mayu, 2019, bayan ya shafe shekaru 35 yana hidima ga hukumar ‘yan sanda da kasa baki daya.

CP Iliyasu, wanda aka turo daga shelkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, ya kasance Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ogun daga shekarar 2016 zuwa watan Junairun 2019.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: