An Sace Mai Shirya Fim Din Hausa Salisu Mu’uzu.

 

Mutanen wadanda ba a gane suba sun sace shahararren mai shirya fina finan hausa da wasu mutane biyu.

Majiyar mu tace an sace sune a kauyen saya a karamar hukumar Bassa ta jahar filato ranar alhamis a kan hanyar su daga jos zuwa Kaduna bayan halartar taron bankin matsakaita da kananan masana’antu a Kaduna.

Idan za a iya tunawa Salisu Mu’azu shine shugaban na hotuna masu motsi mai suna (MOPPAN)Wanda ya shahara kamar manyan jarumai Ali Nuhu da Adam Zango.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Sani Mu’azu Wanda yace tare aka sace su amma saboda shi bashi da lafiya suka barshi ya tafi.

Salisu da abokan sa biyu Dan lami yanke yanke da Bature kan hanyar jos.

Da yake jawabi Sani Mu’azu mun bar Kaduna 4:00 na yamma mun Isa saminaka inda muka tsaya muka buda baki a saminaka tunda muma Azumi.

Sani Mu’azu yace sai suka kora mu daji suna dukana sai kanina yace musu su daina dukana bani da lafiya ya dawo mota.

Inda a safiyar juma’a suka kirana suna bukatar milyan goma kudin fansa

A karshe yana rokon Al’umma da su taya su addua Dan samun kubutar su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.