‘Yan Bindiga Sun Kitsa Munanan Hare Hare A Zamfara

 

….’Yan Bindiga Daďi Sun Kitsa Sabbin Hare Hare A Maberaya

Daga Abdurrahman Abubakar Sada

A Lahadin nan, ‘yan bindiga sun afkawa mutanen garin Maberaya, sai ba su samu nasara (an gargaďe su).

Haka zalika shekaran jiya Talata sun kara dawowa, sun shiga garin Maberaya da safe, sun shiga da yamma. Sai dai a harin shekaran jiyar ne suka samu nasarar kashe mutum uku, suka raunata biyu.

Dukkkanin wadannan munanan hare hare, an kitsa su ne a garin Maberaya da ke karamar Shinkafi, a cikin jihar Zamfara.

Wallahi kullum haka muke kwana haka muke tashi, babu natsuwa babu kwanciyar hankali.

Amma duk da haka saboda tsabar wauta, wasu wawaye ke yada cewa an samu zaman lafiya. Allah ya isa!

Allah ya kawo mana karshen wannan ibtila’i, ya kawar mana da wawayen wakilai.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.