Wata Kotu Ta Sake Rushe Masarautun DA Gwamnatin Kano Ta Samar

Mako guda, bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya dake karamar hukumar Ungogo a Kano ta yanke na rushe karin masarautun yanka hudu da gwamnatin jihar Kano ta samar, sai gashi wata kotun tarayyar dake sakatariyar Audu Bako ta sake yanke hukuncin rushe wadannan masarautu.

Wakikin majiyarmu wanda ya halarci zaman kotun na yau 23/Mayu/2019_ yace alkalin kotun mai shari’a AT Badamasi ya yanke hukuncin cewa masarauta daya ake da ita a jihar Kano, wacce ke karkaahin sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Wadanda suka shigar da karar dai sune Yusuf Nabahani (Madakin Kano),Abdullahi Sarki Ibrahim (Makama Kano),Bello Abubakar (Sarkin Dawaki Mai Tuta) and Mukhtari Adnan (Sarkin Ban Kano).

Daga nan mai shari’ar ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Yuni mai kamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.