Duk Abinda Ya Shafi Masarautar Kano, Ya Shafi Mabiya Darikar Tijjaniyya Na Nijeriya Ne Baki Daya, Inji Sheik Dahiru Bauchi

 

Ga yadda hirar ta kaya tsakaninsa da ‘yan jarida:

Me za ka ce game da raabaa masarautar jihar Kano?

Duk abinda ya shafi Kano ya shafi dukkaninmu ‘yan Tijjaniyya na Nijeriya.

Turawa sun zo sun ci kasar nan, sun shekara 60 suna shegantakarsu amma ba su taba fadar Kano ba.

Bayan su ‘yan siyasa sun gaje su aka samu gwamnonin siyasa wajen guda bakwai a Kano, sannan aka samu gwamnonin mulkin soja wajen guda tara a Kano, duk dai wadannan ba su nemi cin mutunci da kekketa sha’anin fadar Kano ba, sai wannan karon aka samu.

Amma ba don an ce kotu ta riga ta dakatarda maganar ba, da na yi niyyar zan yi jaje ga dukkan ‘yan Tijjaniyyar Najeriya akan abinda ya same mu, domin muhimmancin Kano.

Saboda haka haduwar Shehu da Kano, haduwar mu da Kano, duk mutanen da yake saduwa da su a Kano, yana daukar su ne kamar mutanen Kano. Hakanne yasa muke damuwa akan matsalar fadar Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa al’umma za ta amfana da raba masarauta da aka yi. Ka gamsu da wannan bayanin?

Jama’ar Kano sun ce ba sa so. Masarauta sun ce ba sa so. To wa aka yi wa? Idan dai alkairi ne, wa aka yi wa?

Akwai wani karin bayani da za ka yi akan harkar tsaro a Nijeriya?

Halin da kasa take ciki ba shi da kyau. Amfanin gwamnati shine ta tsare rayukan mutane kada a hallakar dasu. Ta kuma tsare dukiyoyin mutane kada a salwantar, ta tsare gabobin mutane kada a zubar da jinin su. Sannan kuma ta tsare mutuncinsu, idan gwamnati ta addini ce a tsare masu addininsu.

To amma yanzu duk wadannan abubuwa da na lissafo sun zuba a kasa, ana karkashe mutane babu iyaka, ana kokkona musu dukiyarsu, ana kwakkwashe musu dukiyarsu, babu zaman lafiya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.