An Kashe Naira Biliyan 1.5 Wajen Sayen Iccen Kabari A Jihar Bauchi – Aminu Tukur

 

Naira Biliyan Daya Da Miliyan Dari Biyar (1.5b) aka kashe domin sayen Iccen Makabarta

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Lere Bula a karamar hukumar Tafawa Balewa Hon. Aminu Tukur ya ce naira Biliyan daya da miliyan Dari biyar (1.5b) ne aka kashe domin siyen iccen makabarta da ake rufe mutane a jihar Bauchi.

Aminu yayi wannan magana ne a lokacin da yake hira da ‘yan jaridu a jihar Bauchi jim kadan bayan ficewar sa daga jam’iyyar APC inda yace “Naira Biliyan daya da miliyan Dari biyar (1.5b) ne aka kashe domin siyen iccen makabarta da kuma likafani na miliyan Dari takwas da sittin.”

Yace wanan al’amari ya faru ne a cikin shekaru hudu na mulkin gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar na jihar Bauchi.

Daga Jaridar Mikiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.