‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa Kai 5 A Karamar Hukumar Faskari, Ta Jihar Katsina

 

Wasu ‘yan Bindiga sun kashe ‘yan Vigilantee Biyar a wani Farmakin ba za ta da suka kai wani Kauye da ke Karamar Hukumar Faskari, a jihar Katsina, ranar Talata.

Mai Magana da Yawun ‘Yansandan Jihar SP Gambo Isa, ya tabbatar da haka ga Manema Labarai a jihar ta Katsina.

Gambo ya ce, Harin ya Afku ne a Kauyen Sabon Layi da ke Karamar Hukumar inda “Yan sakai” suka yo ayari domin yin fito na Fito da ‘Yan Bindigan yankin.

Ya cigaba da cewa Maharan sun kashe Mutanen Biyar ne a yayin da suke Musayar Wuta a cikin Dajin a yunkurin su na kawo karshen wannan ta’addanci.

Kakakin ‘Yansandan ya cigaba da cewa muna kan Binkice kuma nan ba da jimawa ba za mu kama wadanda suka yi wannan aika aika, inji shi.

NAN

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.