Wai Kuwa Kun San Har Yanzu Surukin Dogarin Buhari Shuru Sama Ko Kasa Makwanni Uku Kenan

 

Wai kuwa kun sami labarin har yanzu surukin Dogarin Buhari da aka sace har yanzu Shiru sama ko kasa babu amo babu labari, kuma maganar da ake makwanni uku kenan.

Idan baku manta ba an sace magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, wanda shine surukin Dogarin Shugaban kasa Muhammad Buhari, a garin Daura bayan sun fito sallar Magariba, makwanni uku kenan.

Zuwa yanzu bamu iya samun rahotan Jami’an tsaro kan wadanne irin matakai suke kan dauka na ganin an dawo da shi gida ba.

Jaridar Dimokaradiyya ta ruwaito cewa Sai dai bayan masu garkuwan sun sace shi, mun sami labarin Kwamishinan Yan sandannJihar Katsina, Sanusi Buba,ya koma Daura da aiki kwatakwata.

Har ila yau mun kuma samun labarin cewar Jami’an tsaro suna daukar matakan da suka dace don ganin an dawo da shi gida.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: