Arangama Tsakanin Masu Zanga-zanga Da Jami’an Tsaro Ta Yi Sanadiyyar Asarar Rai Daya Da Jikkata Wasu A Jihar Katsina

 

Daga Zubairu Haruna Tela Madogara

A yammancin jiya ne zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Batsari bayan kawo gawawwakin mutane 13 da ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Yargamji dake a karamar hukumar ta Batsari.

Jami’an tsaro sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen dakile zanga-zangar wanda har ya kai ga sanadiyyar asarar rai da kuma jikkata wasu.

Karamar hukumar Batsari tana fuskantar matsalar tsaro, inda ‘yan ta’adda ke cin karen su ba babbaka.

Allah ya kawo mana karshen wannan musiba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.