Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Ta Haramta Rufe Hanyoyi A Lokacin Ibada

 

Wannan kudirin dai kai tsaye ya shafi manyan majami’u da kuma manyan masalatai da su ke shingaye kan hanyoyi a ranakun Juma’a da Lahadi da sauran ranaku a lokacin da su ke tsaka da gudanar da Ibadu.

Kudurin wanda ya shiga karatu na biyu da na uku ya samu amincewar ‘yan majalisar jihar ne a zaman da majalisar ta gudanar a ranar Larabar makon jiya, inda suka yi dokar da sauran dokoki guda biyu.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Honorabul Tijjani Aliyu shine ya gabatar da kudurin a kwaryar majalisar wacce ta samu marawar baya daga dan majalisar da ke wakiltar Warji Hon, Yunusa Ahmed.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Kawwa Shehu Damina ya baje kudirin a kwaryar majalisar domin neman amincewar mambobin majalisar, kudirin ya shiga karatu na daya da na biyu har zuwa na uku ba tare da kushewar wani daga cikin ‘yan majalisun ba, A bisa haka ne suka amince da wannan kudirin.

Kakakin majalisar ya nemi gwamnan jihar da ya gaggauta sanya hanu kan wannan kudurin domin ya zama doka a jihar ta Bauchi don neman kawo gyara a cikin garin.

Wakilinmu ya shaida mana cewar sashin zartarwa a jihar kadai ake bukata da sanya hanun gwamnan jihar domin wannan dokar haramta kulle hanya a cikin garin ya zama tabbataccen haramun.

Al’umma da daman gaske suna nuna damuwarsu idan ranar Juma’a da Lahadi suka zo a sakamakon rufe hanyoyin da massalatai da cocina ke yi.

A wani bincike mun gano cewar tun a farko-farkon matsalar ‘yan Boko Haram da tashin Bama-Bamai ne masu mallakin cocina da masalatai suka dauka wa kansu kariyan kai daga dukkanin wani hari ko masu kutse ta hanyar kulle hanyoyin shiga garesu a lokacin da suke kokarin gudanar da Ibadunsu.

sai dai kawo wannan lokacin jihar ta samu kwanciyar hankali domin an dau tsawon lokaci ba a samu wani rahoton aukuwar wani abu makamancin wanda ake tsoro ya auku a jihar Bauchi ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.