Jami’an ‘Yan Sanda Sunyi Nasarar Sheke Wanda Ya Jagoranci Garkuwa Da Shugaban UBEC

 

…sun kuma kwamushe ragowar

Rundunar yan sandan Najeriya ta kashe wanda ake zargi da kitsa garkuwa da shugaban hukumar ilimi ta bai daya (UBEC) da ‘yarsa kwanakin baya a hanyar Abuja.

Majiyarmu ta ruwaito a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba ya fitar da yammacin yau Lahadi yace sun kashe shugaban masu garkuwa da mutanen ne jiya Asabar a yayin wata musayar wuta da akayi tsakanin masu garkuwa da mutanen da kuma ‘yan sanda a dajin Rijana.

A ranar 29 ga watan Afrelun da ya gabata ne dai masu garkuwa da mutanen sukayi garkuwa da shugaban UBEC, Muhammed Mahmood da diyarsa a kusa da kauyen Katari dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mba ya kara da cewa shugaban gungun masu garkuwa da mutanen, Suma’ila Sule, wanda akafi sani da SHAHO ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu daga harbin bindigar ‘yan sanda.

Majiyar tamu ta ruwaito ‘yan sandan sun kuma samu nasarar kama wasu daga cikin gungun ‘yan garkuwar da mutanen da suka hada da Musa Hassan (mai shekara 26), da Ya’u Umar (25), da Umar Musa (22) da kuma Muhammad Sani (28) wadanda dukaninsu mazauna kauyen Rijana ne.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.