Bamu Ji Dadin Yadda Ganduje Ya Kekketa Masarautar Kano Ba – Fadar Shugaban Kasa

 

A karon farko tun bayan matakin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya dauka na tsattsaga masarautar jihar Kano, sai gashi gwamnatin tarayya ta fidda martani cikin bacin rai dangane da wannan al’amari.

A yayin wani taron manema labarai da ya gabatar jiya a fadar shugaban kasa, ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad, yace gwamnatin tarayya tayi tsammanin Ganduje zaifi maida hankali akan abinda ya shafi matsalolin da Kano ke fuskanta na shaye-shaye da rashin aikin yi, amma kuma sai gashi ya fake da wannan.

Lai Muhammad yace sunji takaici matuka game da yadda Ganduje ya tasamma ruguza dadadden tarihin jihar Kano na tsawon shekaru saboda wata manufar sa.

Yace gwamnatin tarayya na yin dukkanin mai yiwuwa domin warware wannan al’amari.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.