Babu Niyyar Kara Kudin Man Fetur A Najeriya

DPR tayi karin haske kan batun karin kudin man fetur, Aminu Ibrahim Mr Antai Asuquo, Kwantrola Janar na Sashin Kula da Albarkatun Man Fetur (DPR) na shiyyar Warri, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar yin karin kudin man fetur a halin yanzu.

Asuquo ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin taron bikin ‘Ranar duniya da al’adu da cigaban al’umma’ da aka gudanar a ofishohin DPR da ke sassan kasar nan.

Kwantrolan ya bukaci ‘yan Najeriya su dena damuwa a kan batun karin kudin man fetur inda ya ce yawan damuwan zai iya janyo cikas wurin samar da man fetur din.

Ya kara da cewa akwai man fetur wadatacce kuma farashinsa yana nan a N145 kowanne lita.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.