Ashe Yan Sanda Aka Kashe Ba Kidinafas Ba Da Safiyar Yau Litinin A Jihar Kaduna

 

Rahotanni daga jihar Kaduna suna bayyana cewa mutanen da aka kashe da sanyin safiyar yau a Kawo ba masu garkuwa da mutane bane yan sanda ne.

A safiyar yau din mun wallafa maku labarin yadda mutanen gari suka far wa wasu mutane tare da kashe daya daga ciki sannan suka kona masu mota kafin dakyar yan sanda suka kwaci ragowar daya mutumin.

Lamarin ya kai ga har an samu salwantar rai cikin matasan da suka far wa wadanda ake zargin a lokacinda yan sandan ke kokarin tarwatsa jama’a. Wasu kuma suka raunata a yayinda matasan suka samu nasarar kona motar wadanda ake zargin tare da mutum daya a cikinsu (wanda a yanzu aka gane ashe Dan sanda ne da ya rako mutanen).

A wata sanarwa da basaraken garin ya fitar, Hakimin Kawo, Mai Marta Jibreel Muhammed Magaji yace abu ne ya hadasu da shi mutumin da suka kama suka jefa mota kuma tun daga jihar Lagos suka biyo shi.

Hakimin wanda shine uban kasa kuma wakilin mai martaba sarkin Zazzau, cewa koda suka zo Kaduna domin kama shi mutumin da akayi zargin sun sace, Alhaji Musa sai da suka je suka nemi izini a ofishin yan sanda sannan suka gabatar da kansu kafin suka shiga nemansa tare da yan sanda a cikinsu.

Ga bayanin Mai martaba Jibreel kamar yadda wata sabuwar Jaridar Hausa MANUNIYA ta ruwaito

“Barkan mu da shan ruwa, ina mai amfani da wannan lokaci in jawo hankalin mu akan abinda ya faru yau a Kawo, bisa ga bincike da gaskiyan magana mutanen da aka kashe aka kuma kona masu mota ba masu satar mutane bane (kidnappers).

Sarkin ya cigaba da bayanin cewa “akwai wani bayani dake tsakanin su dashi mutumin (Alhaji Musa), kuma tun daga Lagos suka biyo shi tare da yan sanda kuma sai da suka gabatar da kan su a police HQ (Hedikwatar yan sanda na Kaduna).”

A karshe sarkin ya jawo hankalin jama’a da su guji daukar doka a hannunsu. Ya ce “Don Allah mu kiyaye daukan doka a hannunmu, yaya zamu yi da hakkin wadan da aka kashe ba tare da laifin su ba?”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: