Kano: Har Bature Ya Gama Shegantakarsa A Najeriya Bai Yi Abinda Muke Gani Yanzu Ba – Inji Sheikh Dahiru Bauchi


Fitaccen Malamin addinin Muslunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya magantu da cewa lallai abinda ya faru a Kano na raba masarauta, abin tsoro ne ga mutane, domin ita jihar Kano, jiha ce ba gama garin jihohi ba.

“Abin da ya faru (a Kano) ya tsoratar da mutane, Bature ya ci kasar nan (Najeriya), ya mallaki kasar, har ya gama shegantakarshi da shekara 60 bai taba masarautar Kano da sunan wargazawa ba.”

Sheikh Bauchi yace tun sanda aka fara mulki a jihar Kano da Najeriya, Sarakuna da masu mulkin siyasa, babu wanda yayi wa Kano abinda ake mata yanzu ba.

“Wadanda sukayi sarauta da mulki, anyi gwamnati wajen kusan gwamnati 9 na sojoji, 7 na fafar hula a Kano, amma ba wanda ya tunkari Kano da irin wannan abinda ake tunkartar ayi yanzu, domin Kano ba irin sauran jihohi bace, zan nanata. “

Sheikh ya kara da cewa; yayi niyyar yiwa mutanen jihar Kano jajen abinda ya faru, amma bayan ya samu labarin ruguje Sarakunan da Kotu tayi, yayi farin ciki da jin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.