Ina Tsoron Ranar Da Talakan Najeriya Zaiyi Bore Ya Hambarar Da Gwamnati A Najeriya – Inji Dino Melaye

Dan majalisar dattijai mai wakiltar al’ummar Kogi ta tsakiya Sanata Dino Melaye ya ce yana tsoron ranar da talakawan Najeriya za su fara yiwa shugabanni bore saboda yadda shugabanni ke azabtar da su.

Melaye, ya wallafa wannan furuci ne yau a shafin sa na Tweeter, inda yace “Ina tsoron irin daukar fansa da talaka zai yi a Najeriya, irin haka ya faru a kasashen Rushiya, Faransa da kuma na kwana-kwanan nan a kasar Sudan”

“Kuma hakan ya faru ne sakamakon rashin adalcin da shugabannin kasashen ke yiwa talakan kasar, mu ma yanzu a Najeriya an kamo hanya” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.