Masu Nadin Sarki A Masarautar Kano Sun Maka Ganduje A Kotu

 

Hudu daga cikin manya masu nadin Sarki a masarautar Kano sun mika gwamnan jihar, Dr Ganduje, zuwa Kuliya Manta Sabo akan karin masarautu 4 da yayi a kwanakin da suka gabata.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa masu nadin Sarkin wadanda suka hadar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan, Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Sarkin Dawaki mai tuta, Bello Abubakar da Makaman Kano, Sarki Abdullahi.

Sun bayyana cewa karin masarautu guda 4 da Gandujen yayi, wani mataki ne na ruguza tarihin jihar Kano musamman cire daraja da rage mukaman sauran basarakai dake masarautar.

Masu karar sunce sun barranta da matakin karin masarautun da gwamnatin tayi kuma sun daukin matakin bisa wakilcinsu na gidan Sullubawa, Yolawa da Dambazawa.

Tun dai a ranar 8 ga watan Mayu ne gwamna Ganduje ya rattaba hannu a bisa dokar da majalissar jihar tayi a cikin kwana 2.

Sai dai Gandujen ya ketare wani hukuncin wata babbar kotun tarayyar dake da zama a Ungoggo wacce ta bukacin gwamnatin ta dakatar da nadin tare da kin basu takardun kama aiki a hukumance.

Al’umma dayawa suna fassara karin masarautun bisa kudirin da gwamnan yake dashi na rage darajar Sarki Muhammadu Sunusi II.

Hakan na zuwa ne bayan da tsagin gwamnatin suka zargeshi da goyon bayan jami’iyyar PDP a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *