Kotu Ta Tsaida Ranar Zama Kan Bukatar Dakatar Da Rantsar Da Buhari

 

Babbar kotun sauraron kararrakin zaben ta kasa da ke Birnin Tarayya Abuja, ta tsayar da 22 ga watan Mayun da muke ciki a matsayin ranar da za ta saurari bukatar da aka shigar gabanta, ta neman dakatar da bikin rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu.

Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar HDP, Ambrose Owuru, tare da shugabancin Jam’iyyar ne suka je kotun, inda suke kalubalantar rashin basu damar shiga zaben shugabancin Najeriya da Hukumar INEC ta yi tun a watan Fabarairun da ya gabata.

Wannan sabon yunkuri na kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi, na zuwa ne watanni 2 bayan da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NRM, Usman Ibrahim Alhaji, da na PDP Alhaji Atiku Abubakar suka garzaya gaban kotun.

Inda Usman Ibrahim Alhaji, na Jam’iyyar NRM. ya shigar da karar Shugaba Muhammadu Buhari, da Kuma Alhaji Atiku Abubakar, bisa karya dokar kashe kudade da suka wuce ka’ida a lokacin gudanar da yakin neman zabukansu, tare da bukatar a soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan na Fabarairu.

Lauyan mai shigar da karar, Mista Ofou Ezekiel, ya zargi Shugaba na Najeriya, Malam Muhammadu Buhari, tare da Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da kashe sama da Naira Biliyan 1 a lokacin yakin neman zabensu da suka gudanar, lamarin da ya ce ya sabawa dokar kasa Najeriya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.