Barayin Shanu Sun Yi Garkuwa Da Mata Uku A Shinkafi

 

Daga Abdurrahman Abubakar Sada

A cikin daren asabar din nan (06/Ramadan/1440), barayin shanun nan masu garkuwa da mutane da zubar da jinin al’ummah, sun sake kaddamar da sabon harin garkuwa da wasu mata a garin Shinkafi.

Idan baku manta ba, a daren jiya Jumu’a sun shigo Shinkafi sun yi awon gaba da wasu ‘yan uwa, haka kuma daren asabar din nan sun sake dawowa.

Mafi muni a wannan hari, wadannan mata da aka yi garkuwa da su marayu ne (uwa da ‘ya’yanta).

‘Yan uwa mu kara cire kasala, mu tashi tsaye don tsaron kanmu da muke a kowane dare, domin samun taimakon Allah da wannan. Domin munga amfanin baiwa kai kariya.

Wadannan munanan hare hare duka a unguwar Sabon Garin Shinkafi aka kaddamar da su. Mutanen Sabon Gari ku tashi ku kare kanku.

Addinin Musulunci ma bai yarda ka zauna hanu sake ba, Musulunci ya baiwa kowa damar daukar matakin kare kansa.

Allah ya kara mana tsaro da kariya. Ameen.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: