Na Fi Karfin Sarki Sunusi, Ta Ko Wace Hanya:~Ganduje

 

Shashin Hausa na jaridar Premium Times ya rawaito cewa;

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi ba sa’an Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bane ko a tsarin dokar kasa.

Ganduje ya ce da shugaban karamar hukuma ya kamata yana sa-in-sa ba gwamna ba domin nan ne hurumin sa sannan daidai shi.

Gyara ne da ci gaba muka kawo jihar mu. Muna so mu kusanto da mutane kusa da shugabannin su. Amma ba daukar fansa ba ko kuma bibiyar wani.

Idan ma har zancen ake so a yi ay a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke ba gwamna ba.

Idan ba dun-ba-dun ba, ay da shugaban hukuma ya kamata yake gani idan bukatan haka ya tashi ba gwamna ba domin gwamna ya yi masa nisa. Haka dokar kasa ta gindaya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.