Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Raba Masarautun Kano

 

Babbar kotun Tarayya da ke Zamanta a Unguwar Ungoggo da ke jihar Kano ta amince da wani umurni da ke dakatar da Gwamna Abdullahi Ganduje daga aiwatar da rabe-raben masarautar Kano.

Mista Ganduje ya sanya hannu a wata doka a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu wacce ta samar da Karin masarautu hudu, yunkurin da ake yiwa kallo a matsayin kokarin rage darajar Sarki Sanusi Lamido.

A take lamarin ya dauki wani sabon salon siyasa inda mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party a majalisar dokoki suka bayyana cewa ba a samar da karin masarautun guda hudu yadda ya kamata ba, inda suka zargi majalisar da mafi rinjayenta yan All Progressives Congress da rashin bin ka’idojin majalisar.

Mambobin PDP biyu a majalisar dokokin, ciki harda Shugaban marasa rinjaye, sun bayyana wa majiyarmu cewa sun samu wani umurni daga kotu da ke adawa da samar da sabbin masarautun da maraicen ranar Juma’ar nan 10 ga watan Mayu.

Yan majalisar sunce ba a yi zaman majalisar yadda ya kamata ba kafin aka yi gaggawan gabatar da dokar a ranar Laraba.

Kuna ga Wannan Umarni zai samu Waje kuwa?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.