Shugaban cocin ‘Christ Evangelical and Life Intervention Ministry’, Fasto Yohanna Buru, ya soma rabon hatsi ga Musulmai domin su sami isasshen abinci a watan falala na Ramadan.
Malamin cocin ya ce wannan ne karo na hudu da cocin take rarraba buhunnan hatsi da suran kayayyakin abinci ga tarin masu barace-barace a kan hanyoyi, ‘yan gudun hijira, yaran da ke gidajen marayu da Musulman da ke kulle a gidan yari.
Ya ce suna aikata hakan ne domin karfafa zaman lafiya, zumunci da soyayya a tsakanin mabiya manyan addinan guda biyu.
Da nasa bangaren, shugaban kungiyar mutane masu nakasa, Malam Abdullahi Sama’ila, ya yi wa cocin godiya sakamakon gudunmawar.