Duk wanda yake marmarin Lahira ne zai bi titin Abuja zuwa Kaduna – Inji Sanata

Sanata Ali Ndume yayi kira ga hukumar Jiragen Kasa ta kasa da ta samar wa matafiya mafita game da yadda ake rige-rigen shiga jirgin Kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Ndume ya ce bai sha da dadi ba a jirgin bayan tsayawa da yayi har na tsawon awowi biyu tun daga Abuja zuwa Kaduna. yayi kira ga gwamnati da ta kara yawan taragon jirgin.

” Na isa tashan jirgi a Abuja amma sai aka ce mini wai jirgin ya cika babu tiket sai dai a bani tiket din tsaye. A tsaye haka muka taho har Kaduna. Abin sam babu dadi.

Sanata Shehu Sani na jam’iyyar PRP, dake wakiltan Kaduna ta Tsakiya ya bayyana wa majalisar cewa ana samun wannan cinkoso ne da cikan jirgin saboda rashin tsaro da yayi wa titin Kaduna zuwa Abuja Katutu.

Shehu Sani ya ce titin Kaduna zuwa Abuja ya zama tashin hankali da yana daga cikin manyan titunan kasar nan da bin su ke da hadarin gaske.

Daga nan sai ya jinjina wa gwamnatin da ta yi hubbasan gina wannan titin jirgi daga Kaduna zuwa Abuja.

Da ya ke tofa ALbarkacin bakin sa a zauren majalisar, Sanata James Manager ya ce ” Babu wani titi a kasar nan da ya fi titin Abuja zuwa Kaduna tashin hankali da hadarin gaske. Duk wanda ya gaji da duniya shi ne zai bi wannan titi a yanzu. A dalilin haka ne za ku ga mutum kamar sanata Ali Ndume da kansa shima ya gwammace ya bi jirgi a tsaye da ya tunkari wannan titi.

Sanatocin sun yi kira ga gwamnati da ta karo yawan taragon jirgin domin wadanda suke a yanzu sun yi kadan matuka.

Shugaban Kwamitin sufurin Kasa na majalisar dattawa Gbenga Ashafa ya bayyana wa majlisar cewa gwamnati ta biya kudin wasu taragogi 12 daga kasar Chana.

” Rashin Kudi ya sa ba a iya siyo su da yawa ba. Gwamnati ta siya taragogi sama da 60 ne amma 12 kawai aka iya biya zuwa yanzu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.