Matasan Zamfara Sun Kashe ‘Yan Bindiga A Fadar Sarki


Wasu matasan Karamar Hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara a a Arewa masa yammacin Kasar nan, sun yi wa fadar Sarkin yankin kawanya, in da suka kashe ‘yan bidiga 7 da suka halarci fadar sarkin da nufin tattaunawar zaman lafiya.

Majiyarmu ta RFI Hausa tace, ‘yan bindigar sun halarci fadar ne domin tattaunawar zaman lafiyar bayan jami’an tsaro sun kwace shanunsu a hare-haren saman da jami’an suka kai kan sansaninsu da ke dajin Birnin Magaji.

Hare-haren sojin saman Najeriya sun tarwatsa ‘yan bindigar, yayinda wasu daga cikinsu suka koma cikin gari domin cigaba da rayuwa a bainar jama’a, lamarin da ya jefa tsoro a zukutan al’umma.

Kazalika hare-haren sun tilasta wa ‘yan bindigar barin shanunsu da yawansu ya kai 200, kuma tuni sojoji suka kwashe shanun, in da aka boye su a fadar Sarkin Birnin Magaji kafin daga bisani a tasa keyarsu zuwa birnin Gusau a makon jiya.

A jiya Laraba ne, ‘yan bindigar suka ziyarci fadar sarkin domin ganin sun yi sulhun da zai kai ga mika musu shanunsu.

Sai dai tuni matasan yankin suka yi wa fadar kawanya tare da kokarin kona fadar sarkin, lamarin da ya sa sojoji suka lallashe su.

Matasan sun far wa ‘yan bindigar ne bayan sun fito daga fadar sarkin, kuma nan take suka aika su lahira.

Rahotanni sun ce, sarkin na Birnin Magaji na ziyara a jihar Kaduna lokacin da wannan al’amari ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published.