‘Yan Daba Sun Kashe Ta Akan Wayar Salula

Malama Fauzeeya kenan ‘yar asalin garin Kontagora dake Jihar Neja da wasu ‘yan daba suka hallaka a kan wayar salula kirar iPhone, lamarin ya farune a daren jiya juma’a a garin Zaria dake Jihar Kaduna, kanin mahaifin tane ya labartawa wakilin mu yadda abun ya faru inda yace ” Unguwar da suke an dauke wutan lantarki sai takai cajin wayar ta wurin masu sana’ar cajin waya domin tasamu cajin da zatayi anfani da shi.

Bayan ta karbo wayar tare da wata ‘yar uwarta sai suka ga wasu mutane na bin su, cikin tsoro da firgici suka cigaba da sauri domin su tsere masu inda ‘yan ta’addan suka yi maza suka tare gaban su tare da umartar ta taba su wayar dake hannun ta inda ita kuma ta tsaya musun ba zata bayar ba nan take daya daga cikin ‘yan ta’addan ya zaro wuka ya caka mata wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ta.

Bayanai sun tabbatar da jami’an tsaro na cigaba da bincike domin gano wadanda suka yi wannan aika-aika.

Da fatan Allah ya jikanta da rahama.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.