Kotu Ta Umarci ‘Nigeria Tribune’ Ta Biya Al-Muntada Diyyar Naira Miliyan 50

 

Babbar kotun jihar Kano a karkashin jagorancin Mai shari’a A. T. Badamasi ta umarci jaridar Nigeria Tribune da ta biya cibiyar harkokin addinin Islama ta Al-Muntada Islamic Trust diyyar Naira miliyan 50, saboda bata wa cibiyar suna da jarida ta yi.

Hukuncin ya na kunshe ne a cikin takardar kotun mai dauke da kwanan wata 17 ga Afrilu, 2019.

Alkalin ya amsa bukatun lauyoyin masu karar, wato Naziru Adamu da Barista F. J. Edema, wadanda su ka nemi kotun da ta bi wa cibiyar kadin kagen da jaridar ta yi ma ta a ranar 13 ga Fabrairu, 2012 lokacin da ta wallafa wani labari mai taken ‘Boko Haram Funding Traced To UK, S/Arabia’.

Tun daga wannan lokaci kungiyar ta tsinci kanta a halin batanci da kyama daga abokan huldarta a gida da waje. Don haka ne ta garzaya gaban kotu neman bin kadi.

Kotu ta ce ta umarci wadanda a ke kara, wato jaridar da mawallafinta, Sam Adesua, “da su biya diyyar Naira miliyan hamsin kacal a matsayin rage radadin cutarwar da a ka yiwa masu kara saboda rage mu su kima da su ka yi a idanun mutane masu halaye na kwarai a cikin al’umma,” in ji mai shari’a.

Hukuncin mai sadara hudu ya kara cewa, “an umarci wadanda a ke kara da wakilansu ko a kusa da su da kada su sake buga wani abu makamancin hakan wanda ya shafi batanci a kan cibiyarmasu karar.”

Sannan kuma Mai shari’a Badamasi ya umarci jaridar da ta tabbatar ta rubuta takardar ban-baki ga masu karar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.