Kano Za Ta Aurar Da Mata 1,500 Ga Maza 1,500

 

…za a kashe naira milyan talatin a sadaki

A ci gaba da kokarin tallafawa jama’arsa, ta bangaren raya Sunnar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sahale ga gwamnatinsa za ta yi bikin daura auren mata su Dubu Daya Da Dari Biyar (1,500) ga mazaje Dubu Daya Da Dari Biyar (1,500), wanda za a gudanar a dukkanin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Wannan gagarumi kuma shahararren biki za a yi shi ne Gone Lahadi 5 ga Watan Mayu, 2019, watakila a na gobe Azumin Watan Ramadhan kenan. Kuma an yi kyakkyawan tsari da shiri na gudanar da wannan gagarumin biki cikin tsafta da nutsuwa a dukkan kananan hukumomin.

Haka nan gwamnatin ce za ta biya sadaki na kudi Naira Dubu Ashirin (N20,000) ga kowace amarya a madadin ango. Wanda kudin ya kama Naira Milyan Talatin kenan (N30m), ga daukacin amare 1,500.

Haka nan kuma saboda a saukakawa ma’auratan, gwamnati ta dauki nauyin siyen kayan daki gaba daya tun daga kan gado da madubin daki da durowa, wajen ajiye kaya, da katifa da labule da kuma ledar daki.

Wannan kyakkyawan shiri ya nuna yadda gwamnatin Ganduje ta ke kulawa da jin dadi da kuma walwalar jama’arta. Musamman kan abinda ya shafi magancewa masu bukatar aure samun auren cikin sauki kuma kyauta kamar yadda wannan shirin ya yunkuro zai yi.

Sa’annan kuma za a bayar da kujeru gaba dayansu saboda gwangwajewar ango da amarya. Misali akwai kujera mai wajen zama na mutum uku da kuma ragowar kananan kujeru, kamar yadda a ka saba gani a gidajen amare. Cikin rufin asiri dai da kuma samun nutsuwa.

Akwai kuma shaddodi da za a rabawa angwaye, saboda su yi shigar sababbin kaya a matsayinsu na angwaye. Hakan zai kara ba su damar fitowa fes-fes cikin walwala da annashuwa a fuskokinsu tsakankanin ‘yan uwa da abokai da kuma masu fatan alheri.

Wannan shirin yin wannan gagarumin biki da zai kewaye dukkan kananan hukumominmu tun farko dama ya samu wata kulawa ta musamman daga gwamna Ganduje. Saboda dama can ya kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da wannan abin alheri.

Shi wannan kwamiti kuma ya kunshi mutane kwararru daga bangarori daban-daban. Daga ciki, baya ga malaman Addinin Musulunci, akwai kuma likitoci. Wadanda sun taka rawar gani wajen ganin an duba lafiyar wadannan mutane. Da kuma ganin kowane mutum ya dace da abinda ya zabarwa kan sa ko a likitance ne.

Auwal Wadata Sansan

Anwar Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano ne ya rubuta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.