Wata kotu ta yanke wa wasu matasa da suka yi fyade hukuncin taran N7,000 a Zaria

Hukuncin wani alkalin kotun shari’ar musulunci da ke da zama a Tudun Wada, a Zariya ya kawo cecekuce bayan ya zartar da hukuncin daurin shekara Daya ko kuma biyan taran Nera N7,000 da bulala 20 ga wasu matasa Uku da suka yi wa wasu yara mata Uku masu shekaru 9-10 fyade.

Alkalin kotun, Malam Iliyasu Muhammad Umar ne ya tabbatar da hakan a yayin da ya ke zartas da hukuncin. Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Tudun Jukun da ke cikin garin Zariya, inda matasan Hassan Sulaiman, Ibrahim Usman da Adamu Audu suka tare yaran a hanyarsu na zuwa makaranta. Hassan Sulaiman da Ibrahim Usman sun afka wa ‘yan shekara Tara-Tara yayin da Adamu Audu ya haike wa ‘yar shekara 10.

Da ya ke gabatar da karan, wanda ya shigar da karan, Sajen Adamu Yahaya ya gamsar da kotun da hujjojinsa kwarara da suka tabbatar wa kotun cewa hakika wadannan matasa sun aikata abin da ake tuhumarsu da shi. Inda daga bisani aka yanke musu wannan hukunci.

Sai dai Komishinan mata ta jihar Kaduna, Hafsat Muhammad Baba ta yi watsi da hukuncin kotun, inda ta ce wannan ya saba wa dokar da jihar ta tanadar wa duk wanda aka samu da laifin yin fyade.

Hajiya Hafsat ta bayyana cewa, jihar ba ta yi sassauci ga masu aikata wannan laifi ba, dan haka ta ce sashi 31 cikin babin farko na dokar ya zartas wa duk wanda aka kama da laifin fyade wa yarinyar da ba ta kai shekara 18 ba to zai fuskanci daurin rai da rai a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.