Dalilin Da Ya Sa Aka Daina Jin Duriyata, Cewar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Wakili


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Mohammed Wakili ya shaida wa BBC abin da ya sa aka yi kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.

Ya ce yana nan daram dam kuma suna aikinsu yadda ya kamata.

“A baya an rika jin duriyata saboda lokacin zabe ne,” kamar yadda ya shaida.

“Ana gwagwarmayar neman zabe akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne wanda yake dauke hankalin jama’a.

“Saboda haka yana bukatar a ji tabbacin cewa za a yi lafiya a gama lafiya…wanda yake duk yanzu babu su,” in ji shi.

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata.

Batun shaye-shaye a jihar Kano

CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama ‘yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu’ammali da miyagun kwayoyin sun suaya salo, “amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.