Anyi Allah wadai da Gwamnan Jigawa Badaru

Yau Gwamna Badaru kusan Shekararsa hudu 4 Yana kan Mulki zuwansa Kasar CHINA Goma 14 da Zimmar zai kawowa jahar Jigawa Cigaba AMMA babu abinda ya Tsinanawa jahar

Dan Majalissar Wakilai Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Gumel da Maigatari da Sule Tankarkar da kuma Gagarawa Hon Sani Zorro yayi Kaca kace da Gwamnan jahar Jigawa Badaru

Hon Sani ya zargi Badaru da shegen yawo Musamman yadda yake barin jahar ya tafi kasar CHINA kasuwancinsa AMMA sai ya fake da cewar Masu Zuba jari ya ke tafiya Nema, Zorro yace Yau fiye da shekara 3 Badaru yana kan Mulki amma zuwansa kasar China 14

Bayan haka Hon Sani zorro yayi zargin cewar Badaru ya Kwacewa Talakawa Gonakinsu ya bawa ‘yan kasar China wai da zimmar zasu yi Noman Rage Gashi kuma An Kasa Biyan diyya ga Masu Gonakan yadda ya dace idan sukayi Magana ko kuma Nuna Rashin Amincewa sai akaisu Gidan Yari

Haka zalika Sani Zorro yace Ga Rashin Tsaro da ya fara Damun jahar ta Jigawa Amma shi kullum Gwamna Badaru akan hanyar tafiye tafiye yake, Irin haka ne ke faruwa da Gwamnan jahar Zamfara Abdul’ziz Yari kusan koda Yaushe baya jahar yana Abuja Ga jaharsa Babu zaman lafiya, AMMA bama fatan irin wannan Halin ya faru a jaharmu Jigawa

Menene Ra’ayinku Gamai da zargin da Sani zorro yayiwa Gwamna Badaru?

Leave a Reply

Your email address will not be published.